
Fiye da manyan Janarori 78 za su yi ritaya daga aiki sakamakon nadin sabbin hafsoshin tsaro da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi.
Rahotanni sun nuna cewa sama da Janarori 78 daga cikin jami’an rundunar sojojin Najeriya za su yi murabus, bayan sabbin nade-naden da aka yi a manyan mukaman tsaro kwanan nan.
Jami’an da ritayar ta shafa sun fito ne daga rukuni ajin soji na 39 da 40 na Rundunar Sojojin Kasa, Sojin Sama, da kuma Sojin Ruwa.