Jahar Kebbi Gwamna Nasir Idris Ya Yi Sauye-Sauye a Majalisar Zartarwar Jihar Kebbi
Tuesday, 28 Oct 2025 00:00 am

Nagari Radio

Gwamna Nasir Idris Ya Yi Sauye-Sauye a Majalisar Zartarwar Jihar Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, ya aiwatar da sauye-sauye a cikin majalisar zartarwar jihar, wanda ya shafi wasu daga cikin kwamishinonin da ke cikin gwamnatinsa.

Sauye-sauyen, wanda ke da nufin ƙara inganta gudanar da ayyukan gwamnati da kuma tabbatar da ingantaccen tsarin mulki, ya haɗa da canjin ma’aikatun da wasu kwamishinoni ke aiki a cikinsu.

A cewar wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi, Alhaji Yakubu Bala Tafida, ya fitar, wannan sabon garambawul ɗin zai fara aiki ne nan take, ba tare da wani jinkiri ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa, wannan mataki na cikin shirin Gwamna Nasir Idris na tabbatar da cewa kowane sashen gwamnati yana aiki yadda ya kamata domin amfanin al’umma baki ɗaya.