Jahar Neja Gwamna Bago ya bayar da hutun kwanaki biyu domin zaben kananan hukumomi a Neja
Wednesday, 29 Oct 2025 00:00 am

Nagari Radio

Gwamna Bago ya bayar da hutun kwanaki biyu domin zaben kananan hukumomi a Neja

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bayar da hutun aiki na kwanaki biyu — Alhamis, 30 ga Oktoba, da Jumu’a, 31 ga Oktoba, 2025 — domin bai wa mazauna jihar damar tunkarar zaben kananan hukumomi da za a gudanar a ranar Asabar.

Arewa Updates ta ruwaito cewa, wannan na cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan Jihar Neja, Bologi Ibrahim, ya fitar a ranar Laraba, 29 ga Oktoba, 2025.

Sanarwar ta bayyana cewa Gwamna Bago ya ce ma’aikatan da ke gudanar da ayyukan gaggawa kamar asibitoci, bankuna da jami’an tsaro, ba su cikin waɗanda hutun ya shafa.

Haka kuma, Gwamnan ya yi kira ga jama’ar jihar da su fito cikin natsuwa da kwanciyar hankali domin kada kuri’unsu ga ’yan takarar da suke so, tare da tabbatar da zaman lafiya yayin zaben.