
An kashe kwamandan hukumar yaki da kwacen waya a Kano
Rahotanni da ke shigowa yanzu sun bayyana cewa wasu da ake zargi da ɓata-gari sun kashe kwamandan kwamitin kar-ta-kwana kan yaƙi da kwacen waya (Anti-Phone Snatching) na Jihar Kano, Inuwa Salisu Sharada, a gidansa da ke cikin garin Kano.
Bayanan farko sun nuna cewa marigayi Inuwa Salisu ya rasu sakamakon harin da aka kai masa a gidansa, sai dai har yanzu babu cikakken bayani kan yadda lamarin ya faru.
Hukuma na ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin kisan tare da gano wadanda ke da hannu a cikin wannan aika-aika.