GOBARA A JABI LAKE MALL: An kone dukiya mai yawa ciki har da shagunan Adidas
Thursday, 30 Oct 2025 00:00 am

Nagari Radio

GOBARA A JABI LAKE MALL: An kone dukiya mai yawa ciki har da shagunan Adidas

Wata mummunar gobara ta tashi a Jabi Lake Mall da ke birnin tarayya Abuja, inda ta lashe dukiya mai tarin yawa ciki har da shagunan Adidas da ke cikin ginin.

A cewar sanarwar da mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, DCF P.O. Abraham, ya fitar a ranar Alhamis 30 ga Oktoba 2025, an bayyana cewa gobarar ta samo asali ne daga shagon Adidas, inda wutar ta ci gaba da ƙonewa har na tsawon sa’o’i shida kafin jami’an kashe gobara tare da hadin guiwar sashen kashe gobara na kamfanin Julius Berger su shawo kanta.

Sanarwar ta kuma nuna cewa an yi nasarar dakile yaduwar gobarar zuwa sauran shaguna da wuraren kasuwanci da ke makwabtaka da mall ɗin. An kiyasta cewa an ceci kayayyaki da kimar su ta kai kusan naira biliyan 94 daga cikin jimillar kayayyaki na kusan naira biliyan 100 da ke cikin shagunan kafin gobarar ta tashi.

Hukumar ta shawarci masu shaguna da gidaje da su rika duba kayan lantarki lokaci-lokaci, su kauce wa yawan haɗa layin wuta, da kuma amfani da na’urorin gano gobara don rage yiwuwar faruwar irin wannan hadari a nan gaba.