Jahar Kebbi Yan sanda sun kama wani da ake zargin da fashi da makami, sun kwato babur da aka sace a jahar Kebbi
Friday, 31 Oct 2025 00:00 am

Nagari Radio

‘Yan sanda sun kama wani da ake zargin da fashi da makami, sun kwato babur da aka sace a jahar Kebbi 

Jami’an rundunar ‘yan sandan Jihar Kebbi sun samu nasarar kama wani mutum da ake zargin dan fashi da makami, tare da kwato  babur da aka sace a yankin karamar hukumar Gwandu ta jahar Kebbi.

A cewar rundunar, wannan nasarar ta biyo bayan wani samame da jami’an suka kai, inda suka gano wanda ake zargin da babur ɗin da aka sace. An ce bincike yana ci gaba domin gano sauran abokan harkallar fashin.