
Rahotanni sun bayyana cewa rundunar sojin Najeriya na ci gaba da tsaurara bincike kan sojojin da suka yi yunkurin juyin mulki a ƙasar.
Rahoton jaridar The Cable ya rawaito cewo an sake binciko ƙarin mutum biyu da ake zargi cikin lamarin.
A rahoton jaridar ta ce tun da fari jami’ai 18 ne ake zargi wanda tuni biyu daga cikinsu suka tsere kuma ana kyautata zaton sun bar ƙasar.
Majiyar ta ce Manjo JM Ganaks mai lambar aiki, N/14363 daga Babban Birnin Tarayya (FCT) na daga cikin waɗanda suka tsere da kuma Kyaftin G Binuga, mai lambar aiki N/167722 daga jihar Taraba.