Donald Trump ya kira Najeriya ƙasar da take yi wa Kiristoci kisan gilla
Saturday, 01 Nov 2025 00:00 am

Nagari Radio

A cikin wani saƙo da  shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa a dandalin Truth Social, ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci sama da 3,100 a Najeriya. Sai dai bai bayyana ainihin tushen waɗannan alkaluman ko kuma hujjojin da suka tabbatar da haka ba.

Wannan furuci nasa ya jawo cece-kuce, inda wasu ke ganin yana ƙoƙarin jawo hankalin duniya kan matsalar tsaro da addini a Najeriya, yayin da wasu ke zargin cewa hakan na iya haifar da tashin hankali ko rikicin addini idan ba a yi taka-tsantsan ba.