Abuja Rundunar ƴansandan Nijeriya reshen babban birnin tarayya Abuja ta yi nasarar ceto wasu ƴan ƙasashen waje 23 da aka sace, tare da kama mutum 14 da ake zargi da satar mutanen don kuin fansa.
Saturday, 01 Nov 2025 00:00 am

Nagari Radio

Rundunar ƴansandan Nijeriya reshen babban birnin tarayya Abuja ta yi nasarar ceto wasu ƴan ƙasashen waje 23 da aka sace, tare da kama mutum 14 da ake zargi da satar mutanen don kuin fansa.
 
Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ƴansandan Abujan, Josephine Adeh, a wata sanarwa, ta ce an gudanar da aikin samamen na leƙen asiri ne ranar 22 ga watan Oktoban 2025, a Unguwan Adamu Ruga Fulani Zone-B, Riverside, da ke Ado Mararaba a jihar Nasarawa.
 
“A wata gagarumar nasara kan masu satar mutane don kuɗin fansa da masu safarar mutane, jami’an rundunar ƴansandan babban birnin tarayya sun kama mutum 14 da ake zargi da satar mutane don kudin fansa tare da ceto mutum 23 ƴan kasashen waje da aka yi garkuwa da su”, in ji sanarwar ƴansandan a jiya Jumma’a.
 
Samamen ya biyo-bayan wani rahoto da aka samu ne cewa an yaudari wasu ƴan kasashen waje aka shigo da su Najeriya da nufin za’a samar musu ayyuka masu kyau, amma daga isowarsu sai aka yi garkuwa da su.