Yan Bindiga Sun Sace Mutane 10 a Jihar Kebbi
Tuesday, 04 Nov 2025 00:00 am

Nagari Radio

‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 10 a Jihar Kebbi

Rahotanni daga Jihar Kebbi sun tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga sun sace akalla mutane goma (10) a yayin hare-haren da suka kai kauyukan Tungar Wazga da Unguwar Chiroma, da ke cikin Karamar Hukumar Danko-Wasagu ta jihar.

A cewar sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Nafiu Abubakar, ya fitar, jami’an tsaro sun bi sawun ‘yan bindigar har zuwa kauyen Marina da ke kan iyakar jihar Kebbi da Zamfara.

Lokacin musayar wuta tsakaninsu, ‘yan bindigar sun saki mutane shida daga cikin wadanda suka sace, kafin su gudu da raunuka zuwa cikin dazukan da ke iyakar Kebbi da Zamfara.