
Gwamna Uba Sani Ya Raba Gidaje Dari Ga Matan Da Suka Rasa Mazajensu A Kaduna
Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya kaddamar tare da raba gidaje 100 masu adana makamashi ga matan da suka rasa mazajensu, karkashin shirin Family Homes Funds tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Kaduna. Wannan aikin shi ne na farko irin sa a duk faɗin Najeriya, kuma Kaduna ce ta fara zama matattarar gwaji.
Gwamna Uba Sani ya jaddada aniyar gwamnatinsa wajen faɗaɗa damar samun gidaje masu sauƙin saya ta hanyar haɗin gwiwa da kungiyoyi da kamfanoni masu zaman kansu. Ya kuma bayyana cewa akwai wasu ayyuka makamantan wannan da ake ci gaba da aiwatarwa a sassan jihar.
Ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu saboda hangen nesan sa, da kuma Ministan Tsare-tsare da Tattalin Arziki bisa jagorantar wannan muhimmin shiri da ya kira “tutar bege da ƙarfin guiwa ga matan marayu da iyalai masu rauni.”