
China ta sha alwashin ci gaba da tallafawa Najeriya a fannin tsaro.
Jakadan ƙasar China a Najeriya ya gudanar da ganawa da Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu, a yau bayan wani muhimmin taron dabarun tsaro.
A lokacin ganawar, jakadan ya jaddada cewa ƙasarsu za ta ci gaba da mara wa Najeriya baya wajen yaƙar ta’addanci da tabbatar da zaman lafiya a cikin ƙasar.
Haka kuma, ya bayyana cewa China ba ta goyon bayan kowace ƙasa da ke tsoma baki cikin al’amuran cikin gida na wasu ƙasashe da sunan addini ko kare ‘yancin ɗan adam, tare da nuna adawar ta ga barazanar sanya takunkumi ba tare da wata hujja mai ƙarfi ba.