Masu Garkuwa Sun Nemi Naira Miliyan 200 a Matsayin Fansa Don Sakin Mataimakin Kakakin Majalisar Kebbi – Ya Roki a Sayar da Kadarorinsa Don A Biya
Thursday, 06 Nov 2025 00:00 am

Nagari Radio

Masu Garkuwa Sun Nemi Naira Miliyan 200 a Matsayin Fansa Don Sakin Mataimakin Kakakin Majalisar Kebbi – Ya Roki a Sayar da Kadarorinsa Don A Biya

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Hon. Sama’ila Muhammad Bagudo, wanda aka sace a ranar Juma’a, 31 ga Oktoba, daga gidansa da ke Bagudo, ya bayyana yana magana daga hannun masu garkuwa da shi.

Jaridar Muryoyi ta ruwaito cewa, a cikin wani sautin murya da ke yaduwa a kafafen sada zumunta, Bagudo ya bayyana cewa an riga an tara kusan Naira miliyan 140 don fansarsa, inda ya roƙi wani ɗan majalisa da ya taimaka wajen sayar da motocinsa guda huɗu domin a samu cikon kuɗin da masu garkuwa ke nema kafin su sako shi.

Rahotanni sun bayyana cewa masu garkuwar sun nemi kuɗin fansa fiye da Naira miliyan 200.

Sai dai, wani abokinsa mai suna Malam Abubakar Bagudo ya bayyana cewa har yanzu ba su tabbatar da sahihancin sautin muryar ba, yana mai cewa, “Ba mu san daga inda wannan sautin ya fito ba, kuma ba mu da tabbacin cewa daga mataimakin kakakin ne muryar ta fito.”

Wasu rahotanni kuma sun nuna cewa ana ci gaba da ƙoƙarin tattara kuɗin fansar domin ganin an kubutar da shi cikin gaggawa.