
Gwamnatin Tarayya ta Buɗe Hanyoyin Tattaunawa da Amurka kan Matsayin Najeriya
Bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta ƙasa, Ministan Yaɗa Labarai da Saita Alkiblar Ƙasa, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta buɗe hanyoyin tattaunawa da ƙasashen duniya, ciki har da Amurka, kan matsayin da ta bai wa Najeriya na ƙasa mai damuwa ta musamman.
A cewar Ministan, Gwamnatin Tarayya ba ta son tayar da jijiyar wuya a kan wannan batu, sai dai tana ɗaukar matakai cikin natsuwa da cikakken kishin ƙasa domin kare martabar Najeriya a idon duniya.
Idris ya bayyana cewa gwamnati na ci gaba da yin duk abin da ya kamata wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa tare da tabbatar da zaman lafiya da ‘yancin addini ga kowa da kowa.
Ya ƙara da cewa, Najeriya ƙasa ce mai mutunta addinai, kuma gwamnati na ɗaukar matakan da suka dace don dakile kashe-kashe da rikice-rikice a sassa daban-daban na ƙasar. Duk da matsalolin tsaro da ake fuskanta, in ji shi, gwamnati na aiki cikin natsuwa, jajircewa da ƙwazo don samar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa.