Gwamnatin Jihar Kebbi ta gayyaci mataimakin shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Reverend Femi Olofin, tare da wasu malamai Musulmi domin gudanar da taron addu’a
Sunday, 09 Nov 2025 00:00 am

Nagari Radio

Gwamnatin Jihar Kebbi ta gayyaci mataimakin shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Reverend Femi Olofin, tare da wasu malamai Musulmi domin gudanar da taron addu’a na musamman, da nufin neman taimakon Allah wajen kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ke addabar jihar.

Gwamnatin jihar Kebbi ta shirya wannan taron addu’a a Birnin Kebbi, babban birnin jihar, domin neman zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban jihar, musamman duba da ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a wasu yankuna.

Taron ya samu halartar Gwamna Nasir Idris tare da manyan jami’an gwamnati da shugabannin addinai. A jawabin sa, Gwamna Idris ya bayyana cewa: “A jihar Kebbi, babu bambanci tsakanin Musulmi da Kirista. Muna tashi tsaye wajen roƙon Allah ya ba mu zaman lafiya da tsaro.”

Reverend Femi Olofin ya jagoranci addu’o’in Kiristoci tare da roƙon Ubangiji ya tsare jihar daga ’yan bindiga, garkuwa da mutane, da sauran matsalolin tsaro, yayin da malamai Musulmi suma suka yi addu’a don zaman lafiya da cigaban jihar Kebbi.