An sace ɗaya daga cikin Motocin gwamnan Abba na Jihar Kano a gidan Gwamnati.
Tuesday, 11 Nov 2025 00:00 am

Nagari Radio

An sace ɗaya daga cikin Motocin gwamnan Abba na Jihar Kano a gidan Gwamnati. 

labarin da jaridar Daily Nigerian ta wallafa, an bayyana yadda wani barawo ya kutsa kai cikin gidan gwamnatin Kano (Government House) ta ƙofar Gate 4, inda ya sace wata mota daga cikin jerin motocin rakiyar mataimakin gwamna!

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru a safiyar Litinin, kuma motar da aka sace ita ce Toyota Hilux, daga cikin motocin hadin gwiwa (convoy) da ake amfani da su wajen ayyukan gwamnati.

Wata majiyar tsaro ta tabbatar da cewa barawon ya fita ta babbar ƙofar gidan gwamnati cikin natsuwa, kamar jami’in gwamnati, ba tare da wani tsoro ko cikas ba.
Bayan an lura da bacewar motar, sai aka tsare direban motar mai suna Shafiu Sharp-Sharp, domin bincike da tambayoyi.

Jami’an tsaro sun ce yanzu suna duba CCTV domin gano yadda aka yi aka samu wannan keta tsaro a cikin gidan gwamnati.

Sai dai har zuwa lokacin da Daily Nigerian ta wallafa rahoton, mai magana da yawun Gwamnan Jihar Kano, Sanusi Dawakin Tofa, bai fitar da wata sanarwa ba kan lamarin.