An shiga fargaba da rudani a garin Izom da ke karamar hukumar Gurara, Jihar Neja
Friday, 14 Nov 2025 00:00 am

Nagari Radio

An shiga fargaba da rudani a garin Izom da ke karamar hukumar Gurara, Jihar Neja, bayan wata tankar mai ta fadi kuma ta kama da wuta.

Lamarin ya faru da misalin karfe 8 na dare, inda direban tankar ya rasa iko da motar yayin da yake kokarin kaucewa ramuka a tsakiyar hanya.

Wani mazaunin garin, Mohammed Adamu, ya bayyana cewa ma’aikatan kashe gobara suna kokarin shawo kan wutar da ke ci har zuwa karfe 8:30 na dare. Ya ce babu wanda ya rasa ran sa, amma akwai gidaje kusa da wurin da gobarar ta faru, lamarin da ke kara tayar da hankali.

Har ila yau, gobarar ta haddasa cunkoso a bangarorin biyu na hanyar.
Shugaban Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Abdullahi Baba Arah, ya ce bai samu cikakken bayani kan lamarin ba a lokacin da aka tuntube shi