
Rundunar Yan sandan jahar Kano ta tabbatar da mutuwar wasu matan Aure biyu a Tudun yolo.
Lamarin ya faru ne a unguwar Tudun Yola, inda ake zargin wasu mutane da ba a san ko suwaye ba suka haura gidan, suka sassara daya daga cikin matan. A cewar bayanai, matar ta biyu kuwa ta firgita ta shige wani ɗaki, daga bisani kuma aka zargin an kunna mata wuta har ta rasa ranta. Dukkanin matan dai na auren mutum daya ne.
Mijin matan, Alhaji Ashiru Shuaibu, ya bayyana yadda lamarin ya faru, inda ya kuma yi addu’ar Allah ya taimaka wa jami’an tsaro wajen gudanar da bincike.
Tuni jami’an tsaro, ciki har da ’yan sandan Rijiyar Zaki, suka isa gidan domin gudanar da bincike. Mun tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa