Jahar Kano Sulhun da ake gudanarwa da ƴan bindiga a jihar Katsina shi ne ke janyo hare-haren da ake fuskanta a wasu sassan Kano,
Saturday, 15 Nov 2025 00:00 am

Nagari Radio

Sulhun da ake gudanarwa da ƴan bindiga a jihar Katsina shi ne ke janyo hare-haren da ake fuskanta a wasu sassan Kano, in ji jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Da yake jawabi a taron yaye ɗalibai na Jami’ar Skyline da ke Kano, Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa ya dace gwamnatin tarayya ce ta jagoranci duk wani sulhu, ba wai a bar ƙananan hukumomi su yi hakan su kaɗai ba.

Tsohon gwamnan ya ce ƴan bindiga na kwarara cikin Kano daga Katsina su na kai hare-hare kan jama’a bayan an kulla irin wannan sulhu a wasu yankuna.

“Ina goyon bayan sulhu, amma wajibi ne gwamnatin tarayya ta shiga cikin lamarin. Ba ya da ma’ana ƙaramar hukuma ɗaya ta ɗauki nauyin hakan ita kaɗai, dole ne gwamnati ta tsoma baki,” in ji shi.

Kwankwaso ya kuma roƙi Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya ƙara zage damtse wajen magance matsalolin tsaro a faɗin ƙasar, tare da nuna ƙwarin gwiwa a matsayinsa na babban kwamandan rundunonin tsaro.