
Rundunar ‘yan sandan farin kaya ta DSS a Najeriya ta bayyana cewa ta cafke wani mutum da ake zargi da safarar makamai ga ’yan bindiga a jihar Filato, wadda ke fuskantar rikice-rikicen ƙabilanci na dogon lokaci.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, hukumar ta ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Laraba, bayan samun muhimman bayanan sirri da suka nuna cewa yana da hannu wajen samar wa kungiyoyin ta’addanci makamai da alburusai.
Haka kuma DSS ta ce bincike ya nuna cewa ana amfani da hanyoyin daji da kuma motocin haya wajen boye makaman, domin shigar da su cikin yankunan da rikici ya yi ƙamari a Filato. An ce kama mutumin na iya zama babban ci gaba wajen rage kai hare-haren da ake yawan samu a yankin.
Hukumar ta kuma tabbatar da cewa tana ci gaba da bincike tare da sauran hukumomin tsaro domin gano sauran mutanen da suke da alaka da wannan hanyar safarar makamai.