
Katsina Ta Rufe Duk Makarantun Gwamnati Saboda Matsalar Tsaro
Gwamnatin Jihar Katsina ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun gwamnati da ke fadin jihar, sakamakon ƙarin damuwa game da yanayin tsaro da ke ta ta’azzara a wasu yankuna.
A wata sanarwa da Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare ta fitar, ta umarci iyaye, malamai da sauran jama’a da su bi wannan umarni nan take, domin kare rayuwar ɗalibai da ma’aikata, yayin da hukumomi ke ci gaba da sanya idanu kan al’amuran tsaro a faɗin jihar.
Gwamnatin ta bayyana cewa rufe makarantun ya zama dole ne domin kauce wa duk wata barazana ga rayuka, tare da tabbatar da cewa za ta rika sabunta bayanai idan akwai sabon mataki ko ɗaukaka doka.