Rundunar Yan sanda Rundunar Yan sanda sun gargadi masu shirin yin zanga zangar sace ɗaliban makarantar GGCSS maga a Jahar Kebbi
Saturday, 22 Nov 2025 00:00 am

Nagari Radio

’Yan sanda sun fitar da gargadi ne bayan samun rahoton cewa wasu kungiyoyi na shirin gudanar da zanga-zanga kan sace daliban Makarantar GGCSS Maga da ke Jihar Kebbi.

 Rundunar ta ce ta samu bayanai cewa akwai shirye-shiryen tattara jama’a domin nuna rashin jin daɗi game da lamarin, abin da ’yan sanda suka ce ya bukaci su ɗauki matakin gaggawa don tabbatar da tsaro da kuma kauce wa duk wani abin da zai tayar da tarzoma.

An bukaci jama’a da kungiyoyi su yi hattara, tare da neman su bi doka da oda wajen bayyana damuwarsu, domin gwamnati da hukumomin tsaro na ci gaba da aiki tukuru wajen ganin an kubutar da daliban cikin koshin lafiya.