Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya gudanar da tattaunawa da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, a gefen taron G20 Leaders’
Sunday, 23 Nov 2025 00:00 am

Nagari Radio

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya gudanar da tattaunawa da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, a gefen taron G20 Leaders’ Summit 2025 da ake yi a Johannesburg, kasar Afrika ta Kudu.

Shettima, wanda ya halarci taron a madadin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi wannan ganawa da Macron domin tattauna muhimman al’amuran da suka shafi inganta dangantaka da ƙarfafa haɗin kai tsakanin Najeriya da Faransa.