Gwamna Uba Sani a yanzu haka yana jagorantar wani gaggautaccen taron hadin gwiwa tsakanin Kungiyar Gwamnonin Arewa da Majalisar Shugabannin Gargajiya ta Arewa a gidan Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna, a yayin da matsalolin tsaro ke ci gaba da ta’azzara a y
Monday, 01 Dec 2025 00:00 am

Nagari Radio

Gwamna Uba Sani a yanzu haka yana jagorantar wani gaggautaccen taron hadin gwiwa tsakanin Kungiyar Gwamnonin Arewa da Majalisar Shugabannin Gargajiya ta Arewa a gidan Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna, a yayin da matsalolin tsaro ke ci gaba da ta’azzara a yankin.

Taron, wanda Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ke jagoranta, ya samu halartar bangaren shugabannin gargajiya karkashin jagorancin Sarkin Musulmi, Mai Alfarma Muhammadu Sa’ad Abubakar III. Zaman na cikin sirri, inda aka mayar da hankali kan lalacewar yanayin tsaro a Arewacin Najeriya.

Shugabannin na tattaunawa kan karuwar hare-haren ’yan ta’adda, fashi da makami, garkuwa da mutane, da rikicin manoma da makiyaya — lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane tare da raba dubban jama’a da muhallansu cikin watanni kalilan da suka gabata.