Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya, (NARD), ta dakatar da yajin aikin sai baba-ta-gani da ta fara kwana 29 da suka gabata.
Monday, 01 Dec 2025 00:00 am

Nagari Radio

Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya, (NARD), ta dakatar da yajin aikin sai baba-ta-gani da ta fara kwana 29 da suka gabata.
 
Cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar na ƙasa, Muhammad Sulaiman ya wallafa a shafinsa an X ranar Asabar da daddare ya ce ƙungiyar ta ɗauki matakin ne a zaman majalisar zartarwarta.
 
Muhammad Suleiman ya ce ƙungiyar ta dakatar da yajin ne na tsawon mako huɗu, sakamakon cimma wasu yarjejeniyoyi da gwamnatin Najeriya kan buƙatun ƙungiyar 19.
 
Ya ƙara da cewa ana sa ran kammala cimma manyan batutuwan da suka janyo yajin aikin - irin su biyan kuɗin ƙarin matsayi da bashin albashi da mambobin ƙungiyar ke bin gwamnati da aiwatar da biyan alawus na musamman - nan da mako biyu masu zuwa.
 
Yajin aikin likitocin ya jefa wasu asibitin ƙasar cikin matsaloli daban-daban, inda marasa lafiya ke kokawa da rashin likitoci a wasu asibitocin ƙasar.