
NSA Ribadu: Za a dawo da ɗaliban da aka sace “nan ba da daɗewa ba”
Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, ya tabbatar wa al’ummar Jihar Neja cewa ɗalibai da ma’aikatan makarantar St. Mary’s Co-Education School da aka sace sama da mutum 300 za su koma gida nan gaba kaɗan.
Ribadu ya yi wannan tabbacin ne a yayin wani muhimmin ziyarar aiki da ya kai yankin makarantar a ranar Litinin, inda ya gana da malamai, iyaye, shugabannin al’umma da hukumomin tsaro domin sanin halin da ake ciki da kuma ƙarfafa musu guiwa.
Ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta zage damtse wajen ganin an kubutar da waɗanda abin ya shafa cikin koshin lafiya, tare da tabbatar da cewa ba za a biya kuɗin fansa ba. A cewarsa, an ɗauki matakan haɗin gwiwa na sirri tsakanin jami’an tsaro domin gano matsugunin ’yan bindigar da kuma ceto yaran cikin lokaci.
NSA ɗin ya bukaci iyaye da al’umma su ci gaba da nuna haƙuri da kwarin gwiwa, yana mai jaddada cewa gwamnati “ba za ta huta ba har sai an dawo da kowa lafiya.”
Har ila yau, Ribadu ya bayyana cewa gwamnatin ƙasa tana sake duba tsarin tsaro a yankunan makarantu, musamman ma a arewacin ƙasar, domin hana maimaituwar irin wannan lamari.