Zamu tsaurara matakan tsaro tare da ɗaukar matakan kariya a duk iya kokin jahar Kebbi — in ji Shugaban Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa.
Sunday, 07 Dec 2025 00:00 am

Nagari Radio

Shugabar Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa ta bayyana cewa dalilin da ya sa ta kai ziyarar aiki jihar Kebbi shi ne domin duba yadda ake gudanar da ayyuka a ofisoshin hukumar, tare da tabbatar da cewa an inganta tsaro a iyakokin jihar.

 

Ta ce ziyarar ta kuma haɗa da tattaunawa da jami’an hukumar kan kalubalen da suke fuskanta, da kuma kawo sabbin matakai na ƙarfafa aikin kulawa da shige da ficen jama’a. Haka zalika, ta jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumar da sauran jami’an tsaro wajen yakar ayyukan fasa-kwabri da sauran laifukan da ke da alaƙa da iyaka.