Ministan Tsaro Bello Matawalle Ya Maka Jaridar Mikiya, Sahara Reporters da Sowore a Kotu
Wednesday, 10 Dec 2025 00:00 am

Nagari Radio

Ministan Tsaro Bello Matawalle Ya Maka Jaridar Mikiya, Sahara Reporters da Sowore a Kotu

Babbar Kotun Jihar Kano da ke cikin Sakatariyar Audu Bako ta karɓi ƙarar da Karamin Ministan Tsaro, Hon. Bello Matawalle, ya shigar kan zargin wallafa labarin da ya ce ba shi da tushe balle makama, wanda aka danganta masa.

A cikin sammacin da aka tura zuwa ofishin Mikiya Online News Ltd, an tabbatar da cewa Ministan ya maka:

1. Sahara Reporters


2. Omoyele Sowore


3. Wani mutum da ba a bayyana sunansa ba


4. Mikiya Online News Ltd

 

Matawalle na zargin cewa Sahara Reporters ta wallafa wani rahoto marar tushe, sannan Jaridar Mikiya ta fassara labarin zuwa Hausa ta kuma wallafa shi, abin da ya bayyana cewa na iya shafar martabarsa da aikinsa na gwamnati.

Ministan na neman kotu ta tilasta waɗanda ake ƙara su biya shi diyyar Naira biliyan goma (₦10,000,000,000) kan wannan zargi.

Ana sa ran zaman farko na shari’ar zai gudana a ranar 14 ga watan Janairu, inda ake sa ran bangarorin da ake ƙara za su fara gabatar da hujjojin su a gaban Alƙali.