
Sojojin Najeriya sun ƙara matsa wa Bello Turji, ya shiga tsananin damuwa
Rahotanni daga Daily Trust sun bayyana cewa shugaban ’yan bindiga Bello Turji yana fuskantar mummunan tashin hankali, bayan da dakarun sojojin Najeriya suka zurfafa farmaki har cikin ɓoyayyun mafakansa.
Majiyar tsaro ta shaida cewa jajircewar rundunar soji a hare-haren da suke kai wa maboyarsa a yankin Arewa maso Yamma ta takaita wa Turji hanyoyin tsira, tare da katse masa dama ta samun sadarwa ko taimako daga sauran miyagun abokan aikinsa.
Rahoton ya ƙara da cewa rundunar soji ta ci gaba da gudanar da ayyuka na musamman, ciki har da sintiri ta ƙasa da ta sama, abin da ya jefa Turji da mabiyansa cikin ruɗani, domin an mamaye muhimman wuraren da suka saba ɓuya.
Al’umma na fatan cewa wannan matsin lamba zai haifar da damar kama ko kawar da Turji, wanda aka jima ana zargi da kai hare-hare, garkuwa da mutane da kuma barnata kauyuka da dama.