Yan bindiga a Jihar Zamfara sun kashe Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Bukuyum, Honarabul Mu’azu Muhammad Gwashi, duk da cewa an shafe kusan watanni shida ana riƙe da shi tare da karɓar kuɗin fansar da suka kai Naira miliyan 15.
Thursday, 11 Dec 2025 00:00 am

Nagari Radio

Yan bindiga a Jihar Zamfara sun kashe Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Bukuyum, Honarabul Mu’azu Muhammad Gwashi, duk da cewa an shafe kusan watanni shida ana riƙe da shi tare da karɓar kuɗin fansar da suka kai Naira miliyan 15.

Rahotanni daga yankin sun nuna cewa maharan sun sace Gwashi ne tun watanni shida da suka gabata yayin da yake komawa gida, inda suka riƙe shi a daji tare da neman kuɗin fansa mai tsoka daga iyalansa. Majiyoyi sun tabbatar da cewa duk da an biya kuɗin fansar da ’yan bindigar suka nema, sai dai hakan bai sa su sake shi ba kamar yadda aka zata.

Wata majiya daga cikin iyalansa ta bayyana cewa an samu labarin kashe Gwashi ne bayan tattaunawa ta yi sarkakiya tsakaninsu da maharan, lamarin da ya ƙara tayar da hankula a ƙaramar hukumar da ma jihar Zamfara gaba ɗaya.

Al’ummar Bukuyum da dama sun bayyana alhinin su kan wannan mummunan lamari, tare da kira ga hukumomi da su ƙara tsaurara matakan tsaro domin kawo ƙarshen hare-haren ’yan bindiga da ke addabar yankin.