Wasu Da Ake Zargi Yan Bindiga Ne Sunyi Garkuwa Da Manoma Akalla 11 a Jahar Kaduna
Friday, 12 Dec 2025 00:00 am

Nagari Radio

Wasu Da Ake Zargi Yan Bindiga Ne Sunyi Garkuwa Da Manoma Akalla 11 a Jahar Kaduna

Al'ummar Ungwar Nungu da ke gundumar Bokana a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna sun Shiga fargaba  bayan da wasu ’yan bindiga sukayi garkuwa da mazauna yankin 11 a ranar Asabar yayin da suke dawowa daga gona kinsu.

Wasu Daga cikin Mazauna yankin su bayyana cewa an tare mutanen ne a wata hanyar daji da ke kusa da unguwar da yamma, inda aka tafi da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Lamarin ya tayar da hankulin al'umma ƙauyukan da na kewaye dasu inda iyalan Wadanda akayi garkuwa dasu suka Shiga rudani.

Sai dai kawo wannan lokacin jami'an tsaro yankin Basu ce uffan ba dangane da faruwa lamarin.