
Zaben 2027 shi ne ke tare da ni wajen korar wasu masu rike da mukaman siyasa da ba su kawo wani ci gaba ko amfani wa gwamnati,” in ji Gwamnan Jihar Neja.
Gwamnan ya ce, a zahiri, akwai mutane da dama da ke rike da mukamai a gwamnati amma ba sa taka rawa wajen aiwatar da manufofin da suka dace da ci gaban jihar. Sai dai saboda an shiga wani lokaci na siyasa mai sarkakiya, musamman yayin da ake dab da fara shirye-shiryen babban zaben 2027, gwamnan ya ce yin tsattsauran mataki kan waɗannan mutane na iya haifar da bacin rai ko rikice-rikicen siyasa da za su iya yi wa gwamnati illa.
Ya kara da cewa gwamnatinsa na da cikakken shiri da kudirin sake fasalin mukamai da inganta aikin gwamnati, amma ya bayyana cewa dole ne ya yi taka-tsantsan saboda yanayin siyasar yanzu. Gwamnan ya tabbatar da cewa da zarar an wuce zaben 2027, zai dauki matakan da suka dace domin tabbatar da cewa kowane mukami ya kasance a hannun wanda ya cancanta kuma ke aiki don al’umma, ba don kansa ba.