Gwamnan Jahar Kebbi ya bamu tirela ukku na Shinkafa domin Bukin Kirismati-
Monday, 22 Dec 2025 00:00 am

Nagari Radio

Gwamnan Jahar Kebbi ya bamu tirela ukku na Shinkafa domin Bukin Kirismati- Shugaban Kungiyar Kiristocin Jahar Kebbi 

Shugaban Kungiyar Kiristoci Nijeriya Reshen Jahar Kebbi Ayuba Kanta, yace Gwamnan jahar Kebbi Dr. Nasir Idris ya basu kyautar tirela 3 na shinkafa domin bukin kirismati.

Shugaban yace tirela biyu an turasu yankin kudancin kebbi inda adda yawan mabiya addinin, yayin tirela daya an barta a nan Birnin kebbi.

Ayuba Kanta ya godewa Gwamnan jahar Kebbi akan irin gudunmuwar ya yake ba mabiya addinin a jahar nan.

Ya kara da cewa zasu raba abincin ga mambobinsu, tareda yan gudun hijira da marasa karfi.

Kanta ya jinjinawa gwamnatin jaha akan basu makabarta wanda yace yamzu aiki yayi nisa wurin zagaye makabartan.