Gwamnatin Yobe ta tallafawa kiristoci 7,000 ka yan abinci Saboda bikin Kirsimeti.
Tuesday, 23 Dec 2025 00:00 am

Nagari Radio

Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya raba kayan abinci ga Kiristoci 7,000 mazauna jihar domin murnar bikin Kirsimeti.

A cewar shirin rabon tallafin, kowanne daga cikin waɗanda suka ci gajiyar ya samu buhun shinkafa, kwalin taliya, man girki da garin semovita, domin gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin farin ciki da walwala.

Da yake jawabi a wajen rabon kayan, Sakataren Gudanarwa na Hukumar Kai Tallafin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA), Dakta Mohammed Goje, ya bayyana cewa Gwamna Buni ya yi kira ga mazauna jihar da su ci gaba da rungumar zaman lafiya tare da yin addu’a domin ci gaban Jihar Yobe da Najeriya baki ɗaya.