Gwamnati Ta Ayyana Ƴan Bindiga a Matsayin Ƴan Ta’adda — Idris
Tuesday, 23 Dec 2025 00:00 am

Nagari Radio

Gwamnati Ta Ayyana Ƴan Bindiga a Matsayin Ƴan Ta’adda — Idris

A karon farko a hukumance, Gwamnatin Tarayya ta ayyana masu aikata ta’asa irin su kai hare-hare, satar mutane da garkuwa da su don karɓar kuɗin fansa a matsayin ƴan ta’adda.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a Abuja, yayin da ake yi wa shekarar 2025 bankwana.

Ya ce wannan mataki na gwamnati ya nuna an kai wani sabon mataki na yaki da rashin tsaro, musamman a yankunan da suka fi fuskantar barazanar ’yan bindiga da masu tada ƙayar baya.

Baya ga batun tsaro, Ministan ya kuma yi bayani kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi ci gaban ƙasa, ciki har da makomar sabuwar dokar haraji da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ke shirin aiwatarwa.