
ACP Kundi Dauda Ya Tsallake Rijiya da Baya a Harin Kwanton Bauna a Jigawa
Wani Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda a Jihar Jigawa, ACP Kundi Dauda Abubakar, ya tsira da ransa bayan da ya samu rauni sakamakon harbin kibiya a wani harin kwanton bauna da ’yan bindiga suka kai wa tawagar ’yan sanda.
Harin ya faru ne a yayin da jami’an ’yan sanda ke gudanar da samame a wani maboyar ’yan bindiga da ke yankin Atuman Fulani, a Karamar Hukumar Jahun, bisa bayanan sirri da suka shafi wasu da ake zargi da kai hare-hare a yankin.
A wata sanarwa da rundunar ’yan sandan ta fitar, ta bayyana cewa ACP Kundi ya samu kulawar gaggawa a Babban Asibitin Jahun, kuma yanzu yana samun sauƙi. Rundunar ta kuma ce an harbi wasu daga cikin ’yan bindigar yayin arangamar, amma suka arce da raunuka.
An kuma bayyana cewa jami’an tsaro na ci gaba da bin sawun ’yan bindigar da kuma ƙoƙarin kwato wasu bindigu da suka kasance a hannunsu.