Gwamnan Gombe ya kori mataimakansa na musamman 4 kan dukan wani kansilan
Wednesday, 24 Dec 2025 00:00 am

Nagari Radio

Gwamnan Gombe ya kori mataimakansa na musamman 4 kan dukan wani kansilan

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da sallamar wasu mataimakansa na musamman guda hudu nan take, bayan kammala bincike kan dukan da aka yi wa Kansilan mazabar Shamaki a Karamar Hukumar Gombe, Hon. Abdulrahman Abubakar Sheriff.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya bayyana cewa kwamitin bincike na musamman tare da rahotannin hukumomin tsaro sun tabbatar da rawar da wadannan mataimaka na musamman suka taka, lamarin da ya sa gwamnan ya dauki matakin sallamarsu ba tare da bata lokaci ba.

Mutanen da abin ya shafa sun hada da Adamu Abdullahi Danko, Garba Mohammed Mai Rago, Rabiu Sulaiman Abubakar da Ali Ibrahim Baban Kaya, dukkansu Mataimakan Musamman na biyu a bangarori daban-daban.

Gwamna Inuwa Yahaya ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci tashin hankali, cin zarafin ofis ko duk wani abu da zai iya barazana ga zaman lafiya da amincewar jama’a ba, yana mai tabbatar wa al’ummar Gombe cewa doka, adalci da zaman lafiya za su ci gaba da zama ginshikin mulkinsa.