
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi ta cafke masu garkuwa da mutane, ta kwato makamai.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi ta sanar da kama wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, tare da kwato makamai a hannunsu, yayin wani samame na tsaro da aka gudanar na tsawon mako guda a sassa daban-daban na jihar.
A cewar sanarwar rundunar, an gudanar da wadannan ayyukan ne domin dakile ayyukan ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka, tare da tabbatar da tsaro da zaman lafiya ga al’umma, musamman a lokacin bukukuwan karshen shekara.
Bincike ya nuna cewa an samu nasarar kama wasu daga cikin wadanda ake zargi a yankunan da aka fi fama da matsalar garkuwa da mutane, inda aka kwato bindigogi da sauran makamai da ake amfani da su wajen aikata laifuka.
Rundunar ta bukaci al’umma da su ci gaba da bada hadin kai, tare da bayar da bayanai ga hukumomi kan duk wani motsi da ake zargi, domin kawo karshen barazanar masu laifi a jihar.