
‘Yan Bin-diga Sun Kai Hari Tungar-giwa A Kebbi, Sun Kashe Mutane 3, Sun Yi Garkuwa Da Wasu
Da yammacin jiya, lokacin sallar Isha’i, ‘yan bindiga ɗauke da makamai sun kai mummunan hari ƙauyen Tungar-Giwa, a Ƙaramar Hukumar Shanga ta Jihar Kebbi.
Majiyoyin cikin al’umma sun tabbatar da cewa: mutane uku sun rasa rayukansu, an yi garkuwa da wasu mazauna ƙauyen. Harin ya jefa jama’a cikin firgici da tashin hankali Kamar yadda Shafin Bakatsine ya rawaito.
Abin da ya fi tayar da hankali shi ne, mazauna yankin sun ce Tungar-Giwa na daga cikin wuraren da ake ɗauka masu aminci a baya, ba a saba samun irin waɗannan hare-hare ba.