
Sanata mai wakiltar shiyyar Nasarawa ta Arewa a Majalisar Dattawa, Godiya Akwashiki, ya rasu yana da shekaru 52 a wani asibiti da ke kasar Indiya.
Jaridun Nasarawa Daily News da Blueprint sun rawaito cewa, iyalansa sun bayyana cewa sanatan ya rasu ne a ranar Laraba bayan ya shafe lokaci yana fama da rashin lafiya, lamarin da ya sa aka kai shi Indiya domin samun kulawar lafiya.
Marigayin ya dade yana jinya kafin rasuwarsa, inda mutuwarsa ta jefa al’ummar Jihar Nasarawa da yankin Eggon cikin jimami.
An haifi Godiya Akwashiki a ranar 3 ga Agusta 1973 a garin Angba Iggah da ke Karamar Hukumar Nasarawa Eggon ta Jihar Nasarawa.
Marigayin ya zama sanata a zaben shekarar 2019 a karkashin jam’iyyar APC, sannan aka sake zabar sa a zaben shekarar 2023 karkashin jam’iyyar SDP.
Kafin zamansa sanata, Akwashiki ya rike mukamin mataimakin shugaban Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa da kuma shugaban masu rinjaye a majalisar.