
Me ya sa Æ´an Najeriya ke yawan faÉ—awa tarkon Æ´an damfara a intanet?
Asarar kuɗi da ƴan Najeriya suka takfa a wani tsarin zuba jari mai suna CryptoBank Exchange wanda aka fi sani da CBEX ya ja hankali a ƙasar, musamman a kafofin sadarwa.
Wannan matsalar ta zo ne a daidai lokacin da ƴan ƙasar suke ci gaba da ƙorafi kan tsadar rayuwa da rashin kuɗi, wanda ya biyo bayan janye tallafin man fetur da karyewar darajar naira.
Rahotanni sun ce kuɗin da ƴan Najeriya suka yi asara a tsarin na CBEX sun haura naira tiriliyan ɗaya, wanda hakan ya sa wasu suke mamakin yadda ƴan ƙasar suka iya tara maƙudan kuɗi haka cikin ƙanƙanin lokaci.
Tuni dai Hukumar EFCC da ke yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar ta sanar da fara gudanar da bincike kan lamarin.
Hukumar ta shaida wa BBC cewa ta haɗa hannu da rundunar ƴansanda ta ƙasa da ƙasa wato INTERPOL da hukumar FBI ta Amurka domin yunƙurin gano waɗanda ke da hannu a dandalin na CBEX tare da ganin yiwuwar karɓo wasu kuɗaɗen da suka maƙale.
Domin bayyana fushinsu, wasu matasa sun gudanar da zanga-zanga, inda suka farfasa ofishin CBEX na birnin Ibadan a jihar Oyo da ke kudancin Najeriya.
Sai dai ba wannan ba ne karon farko da Æ´an Najeriya suke faÉ—awa komar masu irin waÉ—annan harkokin na intanet, inda ake yaudararsu da sunan zuba jari domin samun riba mai yawa, amma ashe shigo-shigo ba zurfi ake musu. Da zarar sun rufta, sai a kulle su ruf.
Daga cikin fitattun kamfanonin da suka yi irin wannan harƙallar a Najeriya akwai Mavrodi Mondial Moneybox (MMM) da XIMA FX da MBA forex da kuma a yanzu CBEX.
'Yadda muka tafka asara'
A tsarin, yawanci ana jan hankalin mutane da sunan za su zuba jari kuɗi kaɗan, sai su riƙa samun riba mai yawan gaske, inda ribar take ninka jarin sau biyu ko uku ko ma sama da haka.
Haka kuma waɗanda suka zuba jari a tsarin, ana neman su nemo wasu, su kwaɗaitar da su cewa akwai riba, idan suka yi hakan, sai su samu ƙarin riba na jawo wani ko wasu cikin harkar.
Haka aka yi da Salisu (ba asalin sunansa ba) ya shiga cikin tsarin ta hanyar wani abokinsa, wanda ya ce masa ya shiga "domin akwai tarin alheri" a ciki idan ya zuba jari.
Sai dai a lokacin Salisu bai fahimci abokin ya jawo ba ne domin ya samu riba da shi, inda ya zuba dalar Amurka 100.
"Na shiga tsarin guda uku, akwai wani mai suna Racsteeli da abokina ya turo min, sai na zuba dala 100. Nan na fara ganin riba na taruwa. Har kuɗina ya kai dala 200 na fara murna, kwatsam sai aka wayi gari shafinsu na intanet ba ya shiga. Sai suka ce wai matsalar intanet ce. Muna cikin jiran tsammani, sai muka wayi gari babu ko sisi a asusunmu. Daga baya ma shafin na intanet ya ɓace," in ji shi.
Ya ce bayan Racsteeli ya sake shiga wani mai suna Delhi, inda shi ma ya zuba kuÉ—i dala 2,000, "amma da hankalina ya dawo na cire kuÉ—ina kafin tsarin ya rufta da wasu.
Shi ma wani mai suna Ola, ya faÉ—a wa sashen BBC Pidgin cewa ya rasa kusan naira 450,000 bayan zuba-jari a tsarin na CBEX.
Me ya sa masu damfarar suke samun nasara a Najeriya?
Duk da cewa ba a Najeriya ba ce aka fara harƙallar zambar, hukumomin ƙasar sun daɗe suna jan hankali tare da gargaɗin mutane da su guji faɗawa komar masu shigo musu da damfara da sunan zuba jari.
Hukumar kula da hada-hadar hannayen jari a Najeriya SEC ta ce babban laifi ne yin hulÉ—a da irin waÉ—annan kamfanoni.
Domin jin yadda suke jan hankalin mutane, Dokta Sa'ad Abdussalam, mai kula da ɓangaren tsara dokoki na hukumar ta SEC ya ce lamarin ya faro ne daga ƙasashen waje lokacin da wani da ake kira ponzi ya ƙirƙiri wani tsari ya damfare mutane suka yi asarar kuɗaɗe da yawa.
"Ina tunanin na farko da ya shigo Najeriya shi ne Nospetco da suka ce suna hada-hadar man fetur. Lokacin da hukumomi suka waiwayi abin sai aka lura cewa ba kasuwanci yake yi ba, yana ɗan hada-hadar man da wasu ƙananan kamfanoni. Amma hada-hadar ba ta kai kusan kashi 10 na kuɗaɗen da ya karɓa ba. Amma yana sayan gidaje da motoci yana tafiye-tafiye," in ji shi.
Jami'in ya ce akwai abubuwa da ke tasiri ga samun nasararsu:
- Talauci
- Son zuciya
- Rashin ilimi
- Burin tara arziki a dare É—aya
Ya ƙara da cewa yawancin masu yin harƙallar ƴan Najeriya, "ina ganin MMM ne kawai wani Bature, amma shi ma sai da ya yi amfani da ƴan ƙasar."
Sai dai ya ce yanzu sun ƙara ƙaimi wajen bibiya, "A baya doka ba ta ba mu damar ɗaukar wasu ƙwararan matakai ba. Amma a wata uku da suka wuce, shugaban Najeriya ya sa hannu a sabuwar dokar kafa hukumarmu, kuma a ciki an amince mu bincika masu irin wannan ayyuka, kuma duk aka samu da laifi zai yi aƙalla zaman gidan yari na shekara 20, da tarar miliyan 20, sannan a ƙwace dukiyarsu."
Yadda za a gane tsarin zuba kuÉ—i na bogi
Dokta Sa'ad Abdussalam ya ce matsalar da ake samu ita ce mutane da dama ba su da ilimin tantace haƙiƙanin hada-hadar gaskiya kafin su zuba kuɗinsu.
Ya ce duk wanda ya ce maka za ka samu riba na fitar hankali, "ya kamata ka gane akwai matsala. Ko kuma ka ga ya fito da abu sabo amma sun buÉ—e ofisoshi masu yawa."
Ya ce suna fara bayar da ribar ga waÉ—anda suka fara shiga, inda suke amfani da kuÉ—aÉ—en waÉ—anda suka shigo daga baya, suna biyan waÉ—anda suka fara, kafin su rufe kowa.
A game da hanyoyin tantancewa, jami'in hukumar ta SEC ya ce, "a shafinmu na intanet, idan ka saka sunansu idan suna da lasisi za ka gani. Ko ka tura mana saƙo ta imel ko ka kira ta waya. Idan ka tura mana saƙo ne za mu maka bayani, sannan daga lokacin za mu fara bincike domin raba jama'a da su."
Ya ce akwai bambanci tsakanin rajista da hukumar da ke yi wa kamfanoni rajista da rajista da hukumar hada-hadar kuÉ—i.
Ya ƙara da cewa yanzu sun faɗaɗa ƙoƙarin da suke yi na ɗaukar matakai, musamman wajen wayar da kan mutane, inda ya ce "amma wasu mutanen suna da taurin kai. Kuma duk da haka muna amfani da shafinmu na intanet da na sada zumunta da sauran hanyoyi. Sannan za mu zagaya makarantu za mu sansanonin horar da masu yi wa ƙasa hidima da kasuwanni da masallatai da coci-coci."
A game da ko za a biya mutanen da aka damfara a tsarin CBEX, ya ce za su yi ƙoƙari su kamo mutanen domin su fuskanci hukunci, sai dai ya ce biyansu zai wahala domin babu kuɗin.
"Ina kuɗin yake? Wataƙila dai EFCC da ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro suna da abin da su yi. Abin da ya fi muhimmanci shi ne mu kama mutanen, su fuskanci doka domin ya zama izina."
Abdulrahman Abubakar