Kungiyar Ma'a bota Sauraren Gidan Radion Nagari FM Birnin Kebbi Sun Zabi Shugabannin Riko...

 

Kungiyar Ma'abota Sauraren Radio Nagari FM (watau Nagari FM Listeners Association NALSA) sun zabi shugabannin riko

 

An zabi shugabannin ne a lokacin da membobin kungiyar suka kawo ziyara na musanman a harabar gidan Radiyon dake titin Sir Ahmadu Bello dake cikin garin Birnin Kebbi a ranar Asabar 05/4/2025.

 

A jawabin sa na musanman, Shugaban gidan Rediyon, Iliyasu Abubakar ya nuna jin dadin sa da kafuwar wannan kungiyar Inda yayi alkawali aiki tare da kungiyar domin ilmantar da al'ummar Jahar Kebbi a dukkan fanin rayuwa.

 

Anasu bangaren, membobin kungiyar sun Sha alwashin ci gaba da sauraren gidan rediyo Nagari FM a ko da yaushe.

 

Sun nemi a ware lokaci na musanman domin basu damar bayarda gudumuwar su, bukatar da Shugaban gidan Rediyon Iliyasu Abubakar ya amince da ita.

 

Shugabannin da aka zaba sune:

 

1- Haddabi Mai Kwanfuta Maiyama a matsayin Shugaban kungiya 

 

2- Sani Shalo limanci a matsayin mataimakin shugaba 

 

3- Zulkifilu Usman a matsayin Sakatare 

 

4- Alhaji Shehu a matsayin Ma'aji

 

5- Abubakar Adamu a matsayin jami'in yada labarai 

 

6-shugaban masu bukata (disable) Faruku Makaho Andarai

 

Sai dattawan kungiya 3 da suka hada da Alhaji Shehu Noma, Aliyu Maigishiri da kuma Sarkin Noma

Umar Ahmad

Comment As:

Comment (0)