Yan bindigar da suka yi garkuwa da mutum 28 a yankin Zak, cikin ƙaramar hukumar Wase da ke Jihar Plateau, sun rage kuɗin fansa daga Naira miliyan 42 zuwa Naira miliyan 30, tare da ƙarin buƙatar sabbin babura guda uku.

’Yan bindigar da suka yi garkuwa da mutum 28 a yankin Zak, cikin ƙaramar hukumar Wase da ke Jihar Plateau, sun rage kuɗin fansa daga Naira miliyan 42 zuwa Naira miliyan 30, tare da ƙarin buƙatar sabbin babura guda uku.

Wadanda aka sace sun haÉ—a da maza da mata da yara, kuma an kama su ne a kan hanyarsu ta zuwa taron Mauludi a garin Sabon Layi, lokacin da maharan suka yi musu kwantan bauna suka kuma yi awon gaba da su.

Duk da cewa jami’an tsaro tare da jiragen sama masu saukar ungulu sun bazama domin ceto waɗanda aka sace, maharan sun dage da cewa ba za su sako su ba sai an biya kuɗin da suka nema.

Iyayen gida da dangi na cikin fargaba da damuwa, inda suka bayyana cewa ba su da ƙarfi ko wata damar tara kuɗin da ake buƙata.

Wani mazaunin yankin Zak, Babawo Gwadabe, wanda maharan suka sace ’yan uwansa bakwai, ya ce: “Ko da mun samu tara kuɗin, har yanzu muna cikin fargaba cewa maharan ba za su sako su ba."

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)