
'Ciwon zuciya da hawan jini': Sabbin buƙatun iyayen 'yanmatan Chibok
Abu kamar wasa, Talata 15 ga watan Afrilun nan ne 'yanmatan sakandare ta Chibok ke cika shekara 11 a hannun mayaƙan ƙungiyar Boko Haram mai iƙirarin jihadi.
Â
A irin wannan rana ne a shekarar 2014 'yanbindigar É—auke da makamai suka afka makarantar da ke da nisan kilomita kusan 125 daga birnin Maiduguri na jihar Borno, inda suka sace yaran 276 da tsakar dare.
Â
Satar ɗaliban ce irinta ta farko da aka taɓa gani a Najeriya, kuma tun daga lokacin 'yanbindiga suka mayar da abin sana'a.
Â
Ƙungiyoyin fafutika, da 'yansiyasa, da fitattun mutane sun yi kiraye-kirayen ceto 'yanmatan bisa maudu'in BringBackOurGirls, wadda ta zama ƙungiya kuma take ci gaba da gwagwarmayar nema wa ɗaliban 'yanci.
Â
Â
Har yanzu sama da 80 na hannun waÉ—anda suka sace su bayan gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ta cim ma yarjejeniyar sakin 82 daga cikinsu, da kuma waÉ—anda suka dinga sulalewa da É—aya-É—aya.
Â
Ana ƙiyasta cewa kusan 180 ne suka kuɓuta daga hannun masu garkuwar tun daga lokacin.
Â
"Cikin baƙin ciki, har yanzu babu wani cigaba da aka samu a yunƙurin ceto su," a cewar ƙungiyar fafutika ta BringBackOurGirls cikin wata sanarwa a ranar Talata. "Iyayensu na ci gaba da fata cikin ƙunar zuci."
Â
Wasu daga cikin 'yanmatan da BBC ta tattauna da su a Afrilun 2024 sun bayyana damuwa game da rashin ba su kulawa a wuraren da gwamnati ta tsugunar da su.
Â
"Na yi da-na-sanin gudowa daga dajin Sambisa zuwa Najeriya," a cewar É—aya daga cikinsu wadda muka sakaya sunanta.
Â
"Wani lokacin sai na yi kuka idan na tuna. Sai na tambayi kai na: 'Me ya sa na bar Sambisa na dawo Najeriya don na tarar da wulaƙanci da zagi a kullum?' Ban taɓa fuskantar irin wannan yanayin ba lokacin da nake Sambisa."
Abdulrahman Abubakar