Yadda mutane ke rayuwa cikin fargaba a garuruwan da Boko Haram ke iko da su

A jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, bayanai na nuna cewa akwai wasu yankunan na wasu ƙananan hukumomin jihar da ƙungiyar Boko Haram ko Iswap ke nuna ƙarfin iko.

 

A ƙarshen makon da ya gabata ne Sanata Ali Ndume, ɗan majalisar dattijai daga jihar Borno ya bayyana wa manema labarai a Abuja cewa ƙananan hukumomin jihar uku na cikin irin wannan hali a yanzu haka.

 

Ƙananan hukumomin sun haɗa da Gudumbari da Marte da kuma Abadam.

 

A baya-bayan nan gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya yi ƙorafin cewa hare-haren Boko Haram da Iswap na ƙaruwa a jihar.

 

Yana mai kira ga gwamnatin tarayya ta ɗauki mataki kafin lamarin ya yi ƙamari.

 

Wasu daga cikin al'umomin waɗannan garuruwa sun shida wa BBC cewa sun shafe tsawon fiye da shekara shida suna rayuwa a ƙarƙashin ikon Boko Haram, kuma kowace rana suna cikin fargaba.

 

Wani mazaunin Gudumbari, da ya buƙaci a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro, ya shaida wa BBC cewa tun 2018, ba su ƙara samun taimakon sojojin Najeriya ba.

 

Ya ce suna rayuwa ne ƙarƙashin ikon mayaƙan - waɗanda suka kai hari tare da lalata wani sansanin sojin yankin da ya kamata ya kare ƙauyukan ƙaramar hukumar Gudumbari.

 

"Tun 2018 lokacin da suka lalata sansanin soji, kusan ƙauyuka 10 ne suka faɗa hannun Boko Haram da ƙungiyar Iswap.

 

"A yanzu haka, shalkwatar ƙaramar hukumar Gudumbari ce kawai ke hannun sojoji, amma kusan duka ƙauyukan ƙaramar hukumar na ƙarƙashin ikon ƴanta'addan,'' in ji shi.

 

Ya ce, ''Kullum mutane na cikin fargaba, saboda kodayaushe suna ganin ƴan ta'addan na sintiri da harkokinsu a waɗannan ƙauyuka.''

 

Ya ƙara da cewa Boko Haram da ƙungiyar Iswap na karɓar haraji da kayan abinci daga hannun manoma, saboda galibi al'ummar yankunan manoma ne.

 

"Lokaci zuwa lokaci suna zuwa karɓar haraji, musamman bayan girbe amfanin gona, haka ma suna zuwa karɓar haraji daga hannun mutane.''

 

Ya shaida wa BBC cewa a wasu lokuta sukan hukunta mutanen da suka aikata ba daidai ba.

 

"Idan mutum ya aikata wani laifi, sukan hukunta shi, ciki har da zanewa."

 

Ya ci gaba da cewa a halin da ake ciki yanzu haka babu wanda ya isa ya fita daga ƙaramar hukumar zuwa birnin Maiduguri, saboda matsalar tsaro.

 

"Idan ka ga mutum ya fito daga Maiduguri zuwa Gudumbari, to sai dai idan yana cikin tawagar gwamna ko cikin rakiyar sojoji,'' a cewar mutumin.

 

'Babu kowa a garin Abadam sai sojoji'

A yankin ƙaramar hukumar Abadam kuwa, lamarin ya fi muni saboda kusan duka fararen hula a garin sun tsere, saboda matsalar tsaron.

 

Wata majiya ta shaida wa BBC cewa a yanzu haka in banda sojoji babu wani mutum da ke rayuwa a shalkwatar ƙaramar hukumar.

 

"A yanzu sojoji ne kawai suka rage a shalkwatar ƙaramar huumar saboda kusan kowa ya fice daga garin don tsira da rayuwarsa.''

 

"Kusan rabin mutanen ƙaramar hukumar sun tsare zuwa Jamhuriyar Nijar inda suka zama ƴan gudun hijria, yayin da sauran mutanen suka warwatsu zuwa makwabtan jihohi.''

 

Majiyar ta kuma ce a yanzu mutanen ba su iya bin hanyar zuwa birnin Maiduguri, maimakon haka sun gwammace bin hanyar shiga Jamhuriyar Nijar.

 

'Ko kayan abinci ba ma iya saya sai da rakiyar sojoji'

Can ma a ƙaramar hukumar Marte, mutanen yankin na ci gaba da tsarewa.

 

Wani mazaunin garin, mai suna Babagana Ali, ya ce a yanzu haka babu kowa a tsohon garin Marte.

 

"A yanzu haka babu wani mutum da ya rage a tsohon garin Marte. Galibi sun koma garin Sabon Marte mai nisan kilomita 12 daga tsohon garin.''

 

Ya ci gaba da cewa mutanen da ke zaune a yankin na rayuwa cikin fargabar, saboda a cewar mayaƙan Boko Haram na kai musu hari.

 

"Mutane na rayuwa cikin fargaba saboda lokaci zuwa lokaci mayaƙan na kai musu hari a garin na Sabon Marte da suke ciki a yanzu.''

 

Ya ƙara da cewa wata matsalar da mutanen garin ke fuskanta ita ce ba sa iya fita zuwa garin Dikwa mai makwabtaka domin sayen kayan abinci.

 

"Mutane ba sa iya fita domin sayo kayan abinci, har sai ƙarshen wata lokacin da sojoji za su yi musu rakiya cikin ayari.''

 

Mazauna garuruwan sun yi kira ga gwamnati da sauran mutanen da za su iya taimakawa don kawo musu zaman lafiya a yankunansu.

 

Jihar Borno ta shafe fiye da shekara 15 tana fama da matsalar tsaro mai alaƙa da Boko Haram, inda take kai hare-hare kan jami'am tsaro da fararen hula, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar ɗaruruwan mutane tare da raba dubbai da muhallansu.

Abdulrahman Abubakar

Comment As:

Comment (0)