
Kashe-kashen Filato gazawar gwamnatin Tinubu ce - Ƙungiyar Dattawan Arewa
Kungiyar dattawan Arewacin Najeriya ta bayyana kashe-kashen da ake yi a jihar Filato a matsayin wata alama ta gazawa daga bangaren gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Â
A wata sanarwa da kakakin ƙungiyar Farfesa Abubakar Jika Jiddere, ya fitar ranar Laraba, ya bayyana kashe-kashen da ake yi a jihar Filato a matsayin abin kunya ga kasa kamar Najeriya.
Ya ce, yadda a baya aka kasance cikin hadin kai da zaman lafiya a Nijeriya maimakon haka ya zama wurin zubar da jini da rashin bin doka da oda.
Yawaitan kisan bayin Allah da da ba su ji ba ba su gani ba, ba komai ba ne illa abin kunya ga ƙasa, kuma babu wanda za'a ɗaurawa alhaki face gwamnatin tarayya da ta gaza wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Ƙungiyar ta ce ba za a yarda da irin wannan aika-aikar na kisan gilla da barna ba, ba tare da wani martani mai ma’ana daga wadanda aka daurawa alhakin kare al’umma ba.
Abdulrahman Abubakar