
Ko kun san illar karancin ruwa ga lafiyar Dan Adam?
Ruwa na da matuƙar muhimmanci ga rayuwa. Hukumomin Duniya da dama sun bayar da shawarar cewa mata su riƙa shan aƙalla lita biyu na ruwa a kowace rana yayin da aka buƙaci maza su riƙa shan lita biyu da rabi.
Â
Rashin shan wadataccen ruwa kan haifar da rashin ruwa a jiki, to sai dai shan ruwan da yawa kuma kan zama matsala.
Â
Ruwa shi ke samar da kashi 60 cikin 100 na nauyin jikinmu, yakan shiga cikin ƙwayoyin halitta da gaɓoɓi da jini da kuma hanyoyi masu yawa na jikinmu.
Â
''Ruwa babban sinadari ne'', in ji Dakta Nidia Rodriguez-Sanchez, ƙwararriya a fannin nazarin matsalolin rashin ruwa a jikin ɗan'adam da ke Jami'ar Stirling da ke Scotland.
Â
"Mukan mayar da hankali wajen nau'ikan abinci masu gina jiki da masu bayar da kariya da masu ƙara kuzari da masu ɗauke da sinadarn narkar da abinci, amma ba ma tunani game da ruwan sha wanda kuma shi ne ke ɗauke da muhimman sinadaran rayuwarmu.''
Â
Me zai faru idan ba ku sha isasshen ruwa ba?
Galibi ruwa kan ƙare a jikinmu saboda zufa da muke fitarwa, da fitsari da kuma numfashi.
Â
Domin ci gaba da aiki yadda ya kamata akwai buƙatar maye gurbin ruwan da ake rasawa sanadiyyar waɗannan abubuwa, wani abu da a kimiyyance ake kira ''daidaita ruwa ''
Â
Idan ruwan da muke fitarwa ya fi wanda muke sha yawa, to za a samu rashin ruwa a jikinmu.
Â
Kuma hakan zai haifar da manyan matsalolin lafiya masu yawa.
Â
Alamomin rashin ruwa a jikin É—an'adam
Â
Fitsari mai launin ruwan É—orawa mai warin gaske
Ƙarancin fitsari yadda ya kamata
Jin kasala ko ganda
Yawan jin gajiya
Bushewar baki da laɓɓa da harshe
kwarmin idanu
A lokuta da dama, rashin ruwa a jiki kan haifar da rashin tabbas, yawan bugun zuciya, da kuma ciwo gaɓoɓi a cewa hukumar Lafiya ta Duniya. (WHO).
Â
Kamar yadda kafar BBC ta wallafa