
Tinubu ya dawo Najeriya bayan ziyarar aiki a Paris da London
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan da ya kai ziyarar aiki zuwa Faransa da Birtaniya.
Â
Shugaba Tinubu ya samu tarba daga manyan muƙarraban gwamnatinsa a lokacin da jirginsa ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe, da ke Abuja, ranar Litinin da daddare.
Â
ÆŠaya daga cikin masu magana da yawun SShugaban Najeriyar, Dada Olusegun ya tabbatar da hakan a shafinsa na X inda ya ce "Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Abuja bayan ziyarar da ya kai Paris da birnin London."
Â
Wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatin da suka yi wa Shugaba Tinubu maraba sun haɗa da Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume da Shugaban ma'aikata a fadar gwamnati, Femi Gbajabiamila da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu da Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Â
A ranar 2 ga watan Afirilu, 2025, Shugaba Tinubu ya yi bulaguro zuwa Paris, babban birnin Faransa inda daga can ya riƙa tafiyar da al'amuran mulki.
Â
Sai dai wasu yan Najeriya sun soki matakin inda suke ganin kamata ya yi ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima.
Â
Tafiyar ta Shugaba Tinubu ta kuma janyo suka daga manyan ƴan adawa a Najeriya - Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Jam'iyyar Labour inda suke ganin bai kamata a ce shugaban ƙasar ya kaɗa kai ya fice daga ƙasar ba a daidai lokacin da ake ƙara fuskantar matsalar tsaro a ƙasar.
Â
Sai dai fadar shugaban Najeriyar ta mayar da martani tana karyata raÉ—e-raÉ—in cewa Shugaba Tinubu ya tafi neman lafiyarsa ne.