
'Babu gudu ba ja da baya wajen inganta tattalin arzikin Jihar Kebbi' - Idris Kauran Gwandu
Gwamnan Jihar Kebbi Kwamared Dakta Nasir Idris (Ƙauran Gwandu) ya jaddada ƙudurin sa na cigaba da gudanar ayyukan alheri da cigaban jihar Kebbi ba tare da nuna gajiyawa ba:
Â
Maigirma Gwamnan Jihar Kebbi Kwamared Dakta Nasir Idris Ƙauran Gwandu ya bayyana cewar babu gudu ba ja da baya wajen cigaba da gudanar ayyukan cigaban al'umma da kuma inganta tattalin arzikin Jihar Kebbi.
Â
Haka kuma Gwamnan ya bayyana cewar da yardar Allah zai cigaba da gudanar ayyukan alheri da cigaban al'ummar Jihar Kebbi kamar yadda ya fara tareda tabbatar da yabar mulkin jihar Kebbi cikin yanayi mai kyau da tsari fiye da shekarun baya.
Â
Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Litinin 21/4/2025 a lokacin zaman tattaunawa da Kungiyar Tuntuba ta Dattawan Jihar Kebbi wato Kebbi Elders Consultative Forum wanda ya gudana a kwalejin kimiyya da fasaha ta Waziri Umaru Federal Polytechnic dake cikin garin Birnin Kebbi.
Â
Da yake jawabi a wurin zaman, Maigirma Gwamna Kwamared Dakta Nasir Idris ya bayyana irin yadda ya karbi ragamar mulkin Jihar Kebbi a shekarar 2023 cike da matsaloli da dama inda yace yanzu ya godema Allah ganin mafi yawan matsalolin ya shawo kansu kuma ana cigaba da magance su a hankali.
Â
Haka kuma Gwamnan ya yabawa Dattawan kungiyar bisa irin kyakkyawan shugabanci da suke nunawa da kuma bayarda shawarwari da zasu É—aga darajar jihar Kebbi inda yace kowani É—an jihar Kebbi mai ruwa da tsaki ne akan cigaban jihar.
Â
Gwamnan ya bayyana cewar Gwamnatin sa zuwa yanzu ta ɗaga darajar ɓangaren ilimi wanda shine ginshikin cigaban kowace al'umma.
Â
Haka kuma ya bayyana cewar Gwamnatin sa ta gaji matsaloli da dama wanda kusan babu wani ɓangare da bashi da matsala amma cikin ikon Allah suna samun nasarar magance matsalolin a hankali.
Â
A ɓangaren ilimi, Gwamnan ya bayyana cewar zuwa yanzu, Gwamnatin sa tayi nasarar gyarawa tare da gina sabbin makarantun firamare da sakandare guda 2,023 a fadin Jihar.
Â
Haka kuma yanzu haka akwai makarantu guda 243 sabbi da Gwamnatin Jihar Kebbi take ginawa wanda kuma aka samar musu da isassun kayan aiki na zamani inda kuma ya bayyana cewar Gwamnatin Jihar Kebbi ta kuma amince da sabon mafi ƙarancin albashi na ₦75,000 ga dukkanin malaman makarantar jihar Kebbi.
Â
Haka kuma Gwamnan ya bayyana cewar Gwamnatin sa ta É—auki sabbin malaman makaranta mutum 2,000 domin su cike gurbin waÉ—anda sukayi ritaya ko suka rasu.
Â
Haka kuma Gwamnan ya ƙara da cewar an kara lokacin ritayar malaman makaranta daga shekara 60 zuwa 65 na haihuwa da kuma shekara 35 zuwa 40 na shekarar kama aiki.
Â
Haka kuma Gwamnan ya bayyana cewar Gwamnatin sa tana cigaba da bayar da ilimi kyauta ta hanyar baiwa É—aliban jihar tallafin karatu wato scholarship da biyan kuÉ—in makarantar É—aliban jami'o'i dake karatu a ciki da wajen kasar Najeriya da kuma biyan kuÉ—in jarawabar É—aliban sakandare ta NECO da WAEC dadai sauransu.
Â
Haka kuma an kara adadin kuɗin ciyar da ɗaliban makarantu abinci daga ₦165m zuwa ₦300m domin samar da ingantacce kuma wadataccen abinci ga ɗalibai.
Â
Haka kuma Gwamnan ya bayyana cewar Gwamnatin sa ta gyara tare da É—aga darajar babban birnin jihar da hanyar gyara da gina sabbin hanyoyin cikin garin Birnin Kebbi da kuma sanya fitilun hanya masu amfani da hasken rana a ko'ina a faÉ—in babban birnin jihar Kebbi wato Birnin Kebbi.
Â
Haka kuma ya bayyana cewar irin wannan aikin ana cigaba da gudanar da irinsa a kusan ko'ina a fadin Jihar Kebbi musamman hedikwatar kananan hukumomin jihar.
Â
Haka kuma ya bayyana cewar Gwamnatin sa ta kashe biliyoyin kuÉ—i wajen inganta harkokin noma da samar da abinci a jihar Kebbi ta hanyar samar kayan noma da suka haÉ—a da takin zamani kyauta, injimin ban ruwa mai amfani da hasken rana, iri da magungunan kwari da dai sauransu ga manoman jihar Kebbi kyauta.
Â
Haka a ɓangaren kiwon lafiya, Gwamnan ya bayyana cewar an kashe makudan kuɗaɗe wajen inganta harkokin kiwon lafiya a jihar Kebbi tare da ɗaukar sabbin ma'aikatan lafiya mutum 1,426 da kuma kara albashin ma'aikatan lafiya na jihar ta yadda zaiyi daidai da na ma'aikatan lafiya na Gwamnatin tarayya domin magance matsalolin barin aikin Jiha zuwa na Gwamnatin tarayya saboda bambancin albashi.
Â
Haka kuma ta ɓangaren inganta tattalin arzikin Jihar, Gwamnan ya bayyana cewar ya nemo masu saka hannun jari da dama a bangarori daban-daban domin bunƙasa tattalin arzikin Jihar inda waɗannan kamfanonin zasu saka hannun jari miliyoyin daloli a ɓangarorin tattalin arzikin Jihar Kebbi.
Â
Haka kuma Gwamnan ya bayyana cewar samar da ruwan sha shima an inganta shi a faÉ—in jihar.
Â
Gwamnan ya tabo ɓangarori daban-daban inda yayi bayanin irin ayyukan da Gwamnatin sa ta gudanar na cigaban al'umma.
Â
Daga cikin waÉ—anda sukayi jawabai a wurin taron harda tsohon Gwamnan Jihar kuma Sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya Sanata Muhammadu Adamu Aleiro wanda ya yabawa Maigirma Gwamna bisa irin nasarorin da yake samu wajen É—aga darajar jihar Kebbi a idon duniya.
Â
Sani Twoeffect Yawuri ya wallafa a shafinsa na fesbuk
Â