
Ko sauya sheƙa zai iya durƙusar da jam'iyyar PDP?
Abubuwa na ta sauyawa a siyasar Najeriya, musamman a baya-bayan nan da aka samu yawaitar ƴan siyasa da ke ficewa daga babbar jam'iyyar adawa ta ƙasar - PDP.
Â
Ficewar gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori daga PDP zuwa APC ta sanya a yanzu yawan gwamnonin jam'iyyar sun ragu.
Â
A Litinin ɗinnan ne mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima da shugaban jam'iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje da kuma sauran ginshiƙan jam'iyyar suka karɓi gwamnan.
Â
Wannan ya sanya a yanzu APC ke da gwamnoni uku daga cikin shida a shiyyar Kudu maso kudancin Najeriya, yankin da a baya jam'iyyar PDP ke da ƙarfi cikinsa tsawon shekara 20.
Â
A yanzu jihohin Cross River da Edo da Delta duk sun koma hannun APC, yayin da Rivers da Akwa Ibom da Bayelsa ke hannun jam'iyyar hamayyar ta PDP.
Â
Sai dai wasu rahotannin na cewa akwai yiwuwar wasu gwamnonin na PDP za su sauya sheƙa.
Â
PDP ita ce babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, sai dai rikice-rikicen cikin gida ya yi mata dabaibayi, lamarin da ake ganin ya hana ta taka rawar da ta kamata a ɓangaren adawa.
Â
Haka nan kasancewar É—aya daga cikin manyan Æ´aÆ´anta - Nyesom Wike - a cikin gwamnatin APC ta Bola Tinubu ya sanya wasu ke zargin ta da kasancewa tamkar "wani reshe na jam'iyyar APC".
Â
Duk da cewa wasu manyan ƴan siyasa a Najeriyar sun nuna alamun cewa za su haɗe domin samar da adawa mai ƙarfi a zaɓen 2027, gwamnonin PDP a taron da suka yi na baya-bayan nan sun nesanta kansu daga haka.
Â
Sai dai ficewar da Æ´aÆ´an jam'iyyar ke yi da kuma karkatar da wasu daga cikin jigajiganta, kamar Atiku Abubakar ke yi ga batun haÉ—akar Æ´an hamayya ba abin da jam'iyyar za ta so ne ba.
Â
Shin wace irin illa hakan zai yi wa PDP?
"Tabbas, PDP na neman ta rasa ƙarfinta a Najeriya duba da yanayin yadda jihohin da jam'iyyar ta mallaka a 2015 da kuma yadda suke yanzu," in ji Lekan Ige, masani a fannin siyasa, a wata hira da BBC.
Â
"A shekarar 2015, PDP ta mallaki jihohi 11, amma yanzu, bayan canjin gwamnan jihar Delta, sun rage zuwa 10. Kuma jita-jita na cigaba da yaÉ—uwa cewa gwamnonin Akwa Ibom da Rivers na iya canza jam'iyya su shiga APC nan ba da jimawa ba.
Â
"Akwai wani lokaci a wannan ƙasa da PDP ta shugabanci ɓangaren zartarwa da kuma majalisar tarayya, amma yanzu ta zama jam'iyyar adawa. Saboda haka ta bayyana ƙarara cewa PDP ta rasa ƙarfin ikonta a Najeriya." In ji Ige.
Â
Har wa yau, masanin ya ƙara da bayanin cewa " babbar illar sauya sheƙar ƴan PDP zuwa jam'iyya mulki shi ne yadda abin ke faruwa a daidai lokacin da ya kamata su haɗe kansu su tunkari APC. Amma yanzu a yadda ake tafiya da wuya jam'iyyar ta iya taɓuka wani abin arziƙi a kakar zaɓe mai zuwa ta 2027. Abin da ke nuna ƙarara cewa jam'iyyar ta durƙushe."